Ezekiel 44:3 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sarki kansa ne kaɗai zai zauna a hanyar shiga don yă ci a gaban Ubangiji. Zai shiga ta hanyar shirayin hanyar shiga yă kuma fita a wannan hanya.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَرْكِے نٜىٰ كَطَيْ، ذَيْ عِيَ ظَوْنَاوَا عَثِكِنْتَ يَثِ عَبِنْثِ أَغَبَنْ يَهْوٜىٰهْ ؞ ذَيْ شِغَ تَوَتَ ڧُواْڢَ، يَشِغَ ذَوْرٜىٰنْ ڧُواْڢَرْ غَبَسْ، يَكُمَ ڢِتَ تَهَنْيَرْ دَيَشِغُواْ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai dai ɗan sarki zai zauna a cikinta ya ci abinci a gaban Ubangiji. Zai shiga ta hanyar shirayin ƙofar, ya kuma fita ta wannan shirayi.”