Ezekiel 44:30 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Mafi kyau na nunan farinku da kuma dukan kyautanku na musamman za su zama na firistoci. Za ku ba su rabo na fari na ɓarzajjen hatsinku saboda albarka ta kasance a gidanku.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دُكَنْ نُونً ڢَارِ مَڢِے ݣَوْ نَكُواْوَنٜىٰ إِرِنْ أَمْڢَانِنْ غُواْنَ دَ كُواْوَنٜىٰ إِرِنْ بَيٜىٰ بَيٜىٰنْ دَ كُكَ كَٰوُاْ مِنِ، ذَاسُ ذَمَ نَڢِرِسْتُواْثِے؞ ذَاكُ بَا ڢِرِسْتُواْثِے غَارِنْ دَ عَكَ ݣُوٻَ نَڢَرْكُواْ دُواْمِنْ أَلْبَرْكَ تَكَسَنْثٜىٰ أَغِدَاجٜىٰنْكُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Dukan nunan fari, da kowace hadaya daga dukan hadayunku, za su zama na firistoci. Za ku ba firistoci tumun farinku don albarka ta kasance a gidajenku.