Ezekiel 44:5 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ubangiji ya ce mini, “Ɗan mutum, ka lura sosai, ka saurara sosai ka kuma mai da hankali ga kome da na faɗa maka game da dukan ƙa’idodi game da haikalin Ubangiji. Ka lura sosai da ƙofar shigar haikali da kuma dukan ƙofofin wuri mai tsarki.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَهْوٜىٰهْ يَا ثٜىٰمِنِ «يَا كَيْ طَنْ مُتُمْ، كَلُورَ سُواْسَيْ، كَغَنِ دَݣَوْ، كَكُمَ كَسَ كُنّٜىٰ غَ دُكَنْ أَبِنْدَ ذَنْ ڢَطَا مَكَ غَمٜىٰدَ دُكَنْ ڧَٰعِدُواْدِ دَ دُكَنْ دُواْكُواْكِنْ هَيْكَلِنْ يَهْوٜىٰهْ ؞ كَلُورَ سُواْسَيْ دَ ڧَٰعِدُواْدِنْ یَنْثِنْ شِغَ هَيْكَلِنْ دَ دُكَنْ وَطَنْدَ ذَاعَ يَرْدَ مُسُ سُشِغَ وُرِے مَيْ ڟَرْكِے دَ وَطَنْدَ بَعَيَرْدَ مُسُبَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ubangiji kuwa ya ce mini, “Ɗan mutum, ka lura sosai, ka gani da idanunka, ka kuma ji da kunnuwanka dukan abin da zan faɗa maka a kan dukan ka'idodin Haikalin Ubangiji da dukan dokokinsa. Ka lura sosai da waɗanda aka yardar musu su shiga Haikalin, da waɗanda ba a yarda musu su shiga ba.