Ezekiel 45:1 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“ ‘Sa’ad da kuka rarraba ƙasar gādo, ku miƙa wa Ubangiji rabon ƙasar ya zama yanki mai tsarki, tsawonsa ya zama kamu 25,000 fāɗinsa kuma ya zama 20,000, dukan ƙasar za tă zama mai tsarki.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«سَعَدَّ كُكَ رَبَ ڧَسَا دُواْمِنْ تَذَمَ رَبُوانْ غَادُواْ، سَيْ كُكٜىٰٻٜىٰ وَ يَهْوٜىٰهْ وَنِ سَاشٜىٰنْ ڧَسَا تَذَمَ سَاشٜىٰ مَيْ ڟَرْكِے، ڟَوُانْسَ ذَيْ كَسَنْثٜىٰ كَمُ دُبُو عَشِرِنْ دَ بِيَرْ، ڢَاطِنْسَ كُمَ كَمُ دُبُو عَشِرِنْ ؞ سَشٜىٰنَّنْ دُكَ ذَيْ ذَمَ مَيْ ڟَرْكِے؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Sa'ad da kuka rarraba ƙasar gādo, sai ku keɓe wa Ubangiji wani wuri domin ya zama yanki mai tsarki, tsawonsa zai zama kamu dubu ashirin da dubu biyar [25,000], faɗinsa kuwa kamu dubu goma [10,000]. Dukan yankin zai zama wuri mai tsarki.