Ezekiel 45:15 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A kuma ba da tunkiya daga kowane garke mai tumaki ɗari biyu daga makiyaya da aka yi masa banruwa sosai na Isra’ila. Za a yi amfani da waɗannan don hadayun gari, hadayun ƙonawa da hadayun salama don yin kafara saboda mutane, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
وَنَّنْ عِتَثٜىٰ بَايَرْوَ دَغَ غَرْكٜىٰنْ دَ ذَاكُيِ؞ ذَاكُ بَادَ تُنْكِيَ طَيَ دَغَ ثِكِنْ كُواْوَنٜىٰ غَرْكٜىٰ مَيْ تُمَكِ طَرِے بِيُ نَ إِسْرَٰٓءِيلَ؞ وَنَّنْ عِتَثٜىٰ بَايَرْوَ تَهَدَايَ تَهَڟِ دَ تَڧُواْنَاوَا دَ تَڠَرَنْ زُمُنْثِ دُواْمِنْ طَوْكَرْ أَلْحَكِنْ ذُنُوبِنْ مُتَنٜىٰنَ؞ نِے عُبَنْ‌غِجِ يَهْوٜىٰهْ نَا ڢَطَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Za ku ba da tunkiya ɗaya daga kowane garke mai tumaki ɗari biyu, a cikin Isra'ila. “Waɗannan su ne hadayu na gari, da na ƙonawa, da na salama, domin a yi musu kafara, ni Ubangiji Allah na faɗa.