Ezekiel 45:17 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Zai zama hakkin sarki ne ya tanada hadayu na ƙonawa, hadayu na gari da hadayu na sha a bukukkuwa, Sabuwar Wata da Asabbatai, a duk ƙayyadaddun bukukkuwa na gidan Isra’ila. Zai tanada hadayu don zunubi, hadayu na gari, hadayu na ƙonawa da hadayu na salama don yin kafara saboda gidan Isra’ila.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَمَّا سَرْكِے نٜىٰ يَكٜىٰدَ حَكِّنْ بَادَ هَدَايُ أَ لُواْكَثِنْ بُكُكُوَ دَ نَبِكٍ سَابُوانْ وَتَ دَ رَانَكُنْ هُوتُنَ نَمَكُواْ، وَتُواْ، دُكَنْ بُكُكُوَنْ دَ عَكَ ڟَارَا نَغِدَنْ إِسْرَٰٓءِيلَ؞ ذَيْ تَنَدَ هَدَايُنْ وَنْكٜىٰ ذُنُوبِ دَ نَهَڟِ دَ نَڧُواْنَاوَا دَ نَڠَرَ زُمُنْثِ دُواْمِنْ طَوْكَرْ أَلْحَكِنْ ذُنُوبِ نَغِدَنْ إِسْرَٰٓءِيلَ؞› »
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sarki ne da nawayar ba da hadayun ƙonawa, da na gari, da na sha a lokacin idodi da na amaryar wata, da ranakun Asabar, da lokacin dukan ƙayyadaddun idodin mutanen Isra'ila. Zai kuma ba da hadayu don zunubi da na salama domin a yi wa mutanen Isra'ila kafara.”