Ezekiel 45:19 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Firist zai ɗibi jinin hadaya don zunubi ya shafa a madogaran ƙofar haikali, a kusurwoyi huɗu na gefen bisa na bagade da kuma a kan madogaran ƙofar shiga na fili na can ciki.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ڢِرِسْتِ ذَيْ طِبِے جِنِنْ هَدَايَ تَوَنْكٜىٰ ذُنُوبِ يَشَاڢَ عَكَنْ ڢِرَمْ نَڧُواْڢَرْ هَيْكَلِنْ، يَكُمَ شَاڢَ عَكَنْ ݣُونَ حُطُ نَبَغَدٜىٰنْ دَ ڢِرَمْ نَڧُواْڢَرْ ڢِيلِ نَثَنْ ثِكِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Firist zai ɗibi jinin hadaya domin zunubi ya shafa shi a madogaran ƙofar Haikalin, da kusurwa huɗu na dakalin bagaden, da ginshiƙan ƙofar fili na can ciki.