Ezekiel 45:4 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Zai zama tsattsarkan rabo na ƙasa domin firistoci, waɗanda za su yi hidima a cikin wuri mai tsarki da kuma waɗanda za su zo kusa don su yi hidima a gaban Ubangiji. Zai zama wuri don gidajensu ya kuma zama tsattsarkan wuri saboda wuri mai tsarki.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
وَنَّنْ سَاشٜىٰ ذَيْ ذَمَ سَاشٜىٰنْ دَ عَكَ كٜىٰٻٜىٰ دَ ڟَرْكِے نَڧَسَرْ؞ وُرِنْ ذَيْ ذَمَ رَبُوانْ ڢِرِسْتُواْثِے وَطَنْدَ سُكٜىٰ ذُوَا كُسَدَ يَهْوٜىٰهْ سُنَيِ مَسَ حِدِمَ؞ وُرِنْ ذَيْ ذَمَ وُرِنْ دَ ذَاسُ غِنَا غِدَاجٜىٰنْسُ دَ كُمَ وُرِے مَيْ ڟَرْكِے دُواْمِنْ هَيْكَلِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Wannan yanki shi ne zai zama wuri mai tsarki na ƙasar. Zai zama na firistoci waɗanda suke hidima a cikin Haikali, waɗanda suke kusatar Ubangiji don su yi masa hidima. Wurin zai zama wurin gina gidajensu da kuma wuri mai tsarki domin Haikalin.