Ezekiel 45:7 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“ ‘Sarki zai kasance da fili da ya yi iyaka da kowane gefe na yankin wuri mai tsarki da kuma mallakar birnin. Zai miƙe ya yi wajen yamma daga gefen yamma ya kuma yi wajen gabas daga gefen gabas, yana miƙewa a tsawo daga wajen yamma zuwa wajen gabashin iyaka don yă yi hannun riga da rabon kabilan.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
« ‹ذَاعَكٜىٰٻٜىٰ سَاشٜىٰ بِيُ نَڧَسَرْ دُواْمِنْ سَرْكِے؞ إِيَاكَرْ سَاشٜىٰ طَيَ ذَاتَ ڢَارَ دَغَ غٜىٰڢٜىٰ نَغَبَسْ نَوُرَارٜىٰنْ دَ عَكَ كٜىٰٻٜىٰ دُواْمِنْ ڢِرِسْتُواْثِے دَ لَوِيَاوَا دَ كُمَ بِرْنِ، تَمِيڧٜىٰ حَرْ إِيَاكَرْ غَبَسْ تَڧَسَرْ؞ إِيَاكَرْ سَاشٜىٰ نَبِيُ كُمَ ذَاتَ ڢَارَ دَغَ غٜىٰڢٜىٰ نَيَمَّ تَمِيڧٜىٰ حَرْ تٜىٰكُنْ مٜىٰدِتٜىٰرٜىٰنِيَ، يَدَّ ڟَوُانْسَ ذَيْ يِدَيْدَيْ دَ ڟَوُانْ سَاشٜىٰنْ دَ عَكَ كٜىٰٻٜىٰ دُواْمِنْ ذُرِيَ طَيَ تَ إِسْرَٰٓءِيلَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Ƙasar da take a sashin yankin nan mai tsarki, da hurumin birnin, zai zama na sarki. Zai zama hannun riga da yanki mai tsarki da hurumin birnin a wajen yamma da gabas. Tsawonta zai zama daidai da yanki ɗaya na yankunan kabilan. Za ta miƙe daga yamma zuwa iyakar ƙasar daga gabas.