Ezekiel 46:11 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“ ‘A bukukkuwa da ƙayyadaddun bukukkuwa, hadaya ta gari zai zama efa tare da bijimi, efa da rago, da kuma ’yan raguna da ya ga dama, haɗe da kwalabar mai.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«أَ لُواْكَثِنْ بُكُكُوَ دَ كُمَ سَوْرَنْ لُواْكَتَنْ دَ عَكَ ڟَارَا، هَدَايَ تَهَڟِ وَدَّ ذَاعَيِ تَرٜىٰدَ طَنْ بِجِمِ ذَاتَ ذَمَ عٜىٰڢَ طَيَ نَهَڟِ؞ هَدَايَ تَهَڟِ وَدَّ ذَاعَيِ تَرٜىٰدَ ضَغُواْ ذَاتَ ذَمَ عٜىٰڢَ طَيَ نَهَڟِ؞ يَوَنْ حَڟِ دُواْمِنْ هَدَايَرْدَ ذَاعَيِ تَرٜىٰدَ یَنْ تُمَكِ ذَاسُ ذَمَ بِسَغَ يَرْدَرْ رَنْ مُتُمْ، ذَيْ يِ نٜىٰ تَرٜىٰدَ هِنْ طَيَ نَمَيْ دُواْمِنْ كُواْوَنٜىٰ عٜىٰڢَ نَهَڟِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A lokacin idodi da ƙayyadaddun lokatai, gārin hadayar da za a yi tare da bijimi wajen garwa guda ne, haka kuma na wadda za a yi tare da ragon, na wadda za a yi tare da 'yan ragunan kuwa, sai mutum ya kawo gwargwadon ƙarfinsa. A kuma kawo wajen kwalaba shida na man zaitun domin kowace garwa ta gari.