Ezekiel 46:12 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’ad da sarki ya ba da hadaya ta yardar rai ga Ubangiji, ko hadaya ta ƙonawa ce ko hadayun salama ne, sai a buɗe masa ƙofar da take fuskantar gabas. Zai miƙa hadayarsa ta ƙonawa ko hadayarsa ta salama yadda yakan yi a ranar Asabbaci. Sa’an nan ya fita, bayan kuma ya fita, sai a rufe ƙofar.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«سَعَدَّ سَرْكِے يَكَٰوُاْ هَدَايَ تَيَرْدَرْ رَيْ، كُواْ هَدَايَ تَڧُواْنَاوَا كُواْ هَدَايَ تَڠَرَنْ زُمُنْثِ أَمَڟَيِنْ هَدَايَ تَيَرْدَرْ رَيْ غَ يَهْوٜىٰهْ ، سَيْ عَبُوطٜىٰ مَسَ ڧُواْڢَرْ دَتَكٜىٰ ڢُسْكَنْتَرْ غَبَسْ؞ سَرْكِنْ ذَيْ مِيڧَ هَدَايَرْسَ تَڧُواْنَاوَا، كُواْ هَدَايَ تَڠَرَنْ زُمُنْثِ كَمَرْ يَدَّ يَكَنْيِ أَ رَانَرْ هُوتُ تَمَكُواْ؞ سَعَنً ذَيْڢِتَ، كُمَ بَايَنْدَ يَڢِتَ، سَيْ أَ رُڢٜىٰ ڧُواْڢَرْ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Sa'ad da sarki ya kawo hadayar ƙonawa ko hadayar salama ta yardar rai ga Ubangiji, sai a buɗe masa ƙofar da take fuskantar gabas. Zai kuwa miƙa hadayarsa ta ƙonawa ko ta salama kamar yadda yakan yi a ranar Asabar. Bayan da ya fita, sai a rufe ƙofa.