Ezekiel 46:16 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa in sarkin ya ba wa ɗaya daga cikin ’ya’yansa kyauta daga gādonsa, zai kuwa zama na zuriyar; zai kuwa zama mallakarsu ta wurin gādo.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«إِنْجِنِ عُبَنْ‌غِجِ يَهْوٜىٰهْ ، عِدَنْ سَرْكِے يَيِ وَوَنِ دَغَ ثِكِنْ یَیَنْسَ ݣَوْتَادَغَ ثِكِنْ رَبُوانْ غَادُوانْسَ، ݣَوْتَرْ ذَاتَ ذَمَ غَادُوانْ طَنْسَ كٜىٰنَنْ؞ رَبُواْنَّنْ ذَيْ ذَمَ نَیَیَنْ طَنَّنْ، أَبِنْ مَلَّكَرْسُ تَغَادُواْ كٜىٰنَنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Ni Ubangiji Allah na ce, idan sarki ya yi wa wani daga cikin 'ya'yansa kyauta daga cikin gādonsa, sai kyautar ta zama ta 'ya'yansa, dukiyarsu ce ta gādo.