Ezekiel 46:18 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Kada sarki ya ƙwace gādon mutane, yana korinsu daga mallakarsu. Zai ba wa ’ya’yansa maza gādonsu daga cikin mallakarsa, don kada a raba wani daga mutanena da mallakarsa.’ ”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَرْكِے بَذَيْ ڨُوثٜىٰ رَبُوانْ غَادُوانْ جَمَعَبَ، حَرْ يَكُواْرٜىٰسُ دَغَ غِدَاجٜىٰنْسُ؞ سَيْ يَبَا یَیَنْسَ رَبُوانْ غَادُوانْسُ دَغَ ثِكِنْ أَبِنْدَ يَكٜىٰ نَاسَ كَطَيْ، دُواْمِنْ كَدَ أَ رَبَ جَمَعَتَ دَ مَلَّكَرْسُ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Kada sarki ya ƙwace rabon gādon jama'a, ya hana musu. Sai ya ba 'ya'yansa maza rabon gādo daga cikin abin da yake nasa, amma kada ya ƙwace wa jama'ata abin da suka mallaka har su warwatse.”