Ezekiel 46:19 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’an nan mutumin ya fitar da ni ta ƙofar shiga a gefen ƙofar zuwa tsarkakakkun ɗakuna waɗanda suke fuskantar arewa, waɗanda suke na firistoci, ya kuma nuna mini wani wuri daga can ƙurewar yamma.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَثِكِنْ رُعُيَتَ، سَيْ مُتُمِنْ يَبِے دَنِے تَهَنْيَرْ دَتَكٜىٰ غٜىٰڢٜىٰنْ ڧُواْڢَ مَيْ ڢُسْكَنْتَرْ أَرٜىٰوَ، عِنْدَ جٜىٰرِنْ طَكُنَنْ دَ عَكَ كٜىٰٻٜىٰ دُواْمِنْ ڢِرِسْتُواْثِے سُكٜىٰ، وَطَنْدَ سُكٜىٰ ڢُسْكَنْتَرْ أَرٜىٰوَ؞ عَثَنْ نَغَ وَنِ وُرِے عَ إِيَاكَرْ يَمَّ دَ طَكُنَنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai mutumin ya bi da ni ta hanyar da take gefen ƙofa mai fuskantar arewa, wajen jerin tsarkakakkun ɗakuna na firistoci, waɗanda suke fuskantar arewa. Na kuma ga wani wuri daga can ƙurewar yamma.