Ezekiel 46:2 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sarki zai shiga daga waje ta shirayin hanyar shiga yă tsaya a madogarar ƙofa. Firistoci za su miƙa hadayarsa ta ƙonawa da hadayunsa na salama. Zai yi sujada a madogarar ƙofar hanyar shiga sa’an nan ya fita, amma ba za a rufe ƙofar ba sai da yamma.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَرْكِے ذَيْ شِغَ تَذَوْرٜىٰنْ ڢِيلِ دَغَ وَجٜىٰ، سَعَنً يَڟَيَ كُسَدَ ڢِرَمْ نَڧُواْڢَرْ، سَعَدَّ ڢِرِسْتُواْثِے سُكٜىٰ مِيڧَ هَدَايَ تَڧُواْنَاوَا دَ هَدَايَ تَڠَرَنْ زُمُنْثِ أَمَدَدِنْسَ؞ سَعَنً سَرْكِے ذَيْ رُسُنَ دَ ڢُسْكَرْسَ حَرْ ڧَسَا أَوُرِنْ أَ ڢِرَمْ نَڧُواْڢَرْ يَكُمَ ڢِتَ؞ عَمَّا بَذَاعَ رُڢٜىٰ ڧُواْڢَرْ بَ سَيْ دَ يَمَّ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sarki zai shiga ta ƙofar shirayi daga waje, sa'an nan ya tsaya kusa da ginshiƙin ƙofar. Sai firistoci su miƙa hadayarsa ta ƙonawa, da hadayunsa na salama, shi kuwa ya yi sujada s bakin ƙofar, sa'an nan ya fita, amma ba za a rufe ƙofar ba sai da maraice.