Ezekiel 46:7 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Zai tanada a matsayin hadaya ta gari, efa guda tare da bijimi, efa guda tare da ’yan raguna, da kuma ’yan raguna yadda ya ga dama, tare da kwalabar mai don kowace efa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَرْكِے ذَيْ تَنَدَ عٜىٰڢَ طَيَ نَهَڟِ دُواْمِنْ هَدَايَ تَهَڟِ تَرٜىٰدَ بِجِمِ، ذَيْبَادَ عٜىٰڢَ طَيَ تَرٜىٰدَ ضَغُوانْ، تَرٜىٰدَ یَنْ تُمَكِ كُمَ ذَيْبَادَ حَڟِ بِسَغَ يَرْدَرْ رَنْسَ؞ ذَيْبَادَ هِنْ طَيَ نَمَيْ دُواْمِنْ كُواْوَنٜىٰ عٜىٰڢَ نَهَڟِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Gārin hadayar da za a yi tare da bijimin wajen garwa guda ne, haka kuma gari na wadda za a yi tare da ragon, da gari na wadda za a yi tare da 'yan raguna kuma, zai zama gwargwadon ƙarfinsa. Zai ba da man zaitun wajen kwalaba shida domin kowace garwa ta garin.