Ezekiel 46:9 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“ ‘Sa’ad da mutanen ƙasar suka zo gaban Ubangiji a ƙayyadaddun bukukkuwa, duk wanda ya shiga ta ƙofar arewa don yă yi sujada sai ya fita ta ƙofar kudu; kuma duk wanda ya shiga ta ƙofar kudu sai ya fita ta ƙofar arewa. Ba wanda zai koma ta ƙofar da ya shiga, amma kowa zai fita a ƙofar ɗaura da wadda ya shiga.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«أَ رَانَكُنْ بُكُكُوَنْ دَ عَكَ ڟَارَا، سَعَدَّ مُتَنٜىٰنْ ڧَسَرْ سُكَذُواْ غَبَنْ يَهْوٜىٰهْ دُواْمِنْ يِنْ سُجَّدَ، دُكْ وَنْدَ يَشِغَ تَڧُواْڢَرْ أَرٜىٰوَ دُواْمِنْ يِنْ سُجَّدَ، سَيْ يَڢِتَ تَڧُواْڢَرْ كُدُ؞ وَنْدَ كُمَ يَشِغَ تَڧُواْڢَرْ كُدُ، سَيْ يَڢِتَ تَڧُواْڢَرْ أَرٜىٰوَ؞ دُكْ وَنْدَ يَبِے تَوَتَ ڧُواْڢَ يَشِغَ، إِنْ ذَيْڢِتَ بَذَيْبِے وَنَّنْ ڧُواْڢَرْ بَ، عَمَّا سَيْ يَبِے تَطَيَنْ ڧُواْڢَرْ يَڢِتَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Sa'ad da jama'ar ƙasar sun zo yi wa Ubangiji sujada a lokatan ƙayyadaddun idodi, wanda ya shiga ta ƙofar arewa, sai ya fita ta ƙofar kudu. Wanda kuma ya shiga ta ƙofar kudu, sai ya fita ta ƙofar arewa. Kada kowa ya fita ta ƙofar da ya shiga, amma sai kowa ya fita ta akasin ƙofar da ya shiga.