Ezekiel 47:1 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Mutumin ya komo da ni zuwa mashigin haikalin, sai na kuwa ga ruwa yana malalowa daga ƙarƙashin madogarar ƙofar haikalin wajen gabas (gama haikalin yana fuskantar gabas). Ruwan yana malalowa daga ƙarƙashin gefen kudun haikalin, kudu da bagaden.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ مُتُمِنْ يَكُواْمُواْ دَنِے ذُوَا بَاكِنْ ڧُواْڢَرْ هَيْكَلِنْ، ثَنْ نَغَ ضُوَ يَنَ ٻُلْٻُلُّواْوَ دَغَ ڧَرْڧَشِنْ بَاكِنْ ڧُواْڢَرْ هَيْكَلِنْ ذُوَا وَجٜىٰنْ غَبَسْ، غَمَا هَيْكَلِنْ يَنَ ڢُسْكَنْتَرْ غَبَسْ؞ ضُوً يَنَ ڢِتُواْوَ دَغَ غٜىٰڢٜىٰنْ كُدُ نَبَاكِنْ ڧُواْڢَرْ هَيْكَلِنْ، يَنَ غَنْ‌غَرُواْوَ أَغٜىٰڢٜىٰنْ كُدُ نَبَغَدٜىٰنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ya komo da ni zuwa ƙofar Haikalin, sai ga ruwa yana bulbulowa daga ƙarƙashin bakin ƙofar Haikalin a wajen gabas, gama Haikalin na fuskantar gabas. Ruwan kuwa yana gangarowa daga gefen kudancin bakin ƙofar Haikalin, a kudancin bagaden.