Ezekiel 47:12 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
’Ya’yan itatuwa na kowane iri za su yi girma a kowane gefen kogin. Ganyayensu ba su bushe ba, ba kuwa za su fasa yin ’ya’ya ba. Kowane wata za su ba da ’ya’ya domin ruwa daga wuri mai tsarki yana malalo musu. ’Ya’yansu za su zama abinci, ganyayensu kuma za su zama magani.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَكَنْ كُواْوَنٜىٰ بَاكِنْ كُواْغِنْ، عِتَتُوَ إِرِ إِرِ مَاسُ بَادَ أَمْڢَانِ ذَاسُيِ غِرْمَ؞ غَنْيَيٜىٰنْسُ بَذَاسُ تَٻَ بُوشٜىٰوَبَ، كُمَ عِتَتُوَنْ بَذَاسُ تَٻَ ڢَاسَ بَادَ یَیَبَ، عَمَّا ذَاسُيِ تَبَادَ یَیَ كُواْوَنٜىٰ وَتَ؞ غَمَا ضُوً دَ يَكٜىٰبِے تَغِنْدِنْ عِتَتُوَنْ دَغَ هَيْكَلِنْ نٜىٰ يَٻُلُّواْ؞ یَیَنْ عِتَتُوَنْ عَبِنْثِنٜىٰ، غَنْيَيٜىٰنْسُ كُوَ مَاغَنِنٜىٰ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A kowace gāɓar kogin, itatuwa iri iri na abinci za su yi girma. Ganyayensu ba za su bushe ba, itatuwan kuma ba za su fasa yin 'ya'ya ba, amma su za su yi ta bayarwa a kowane wata, gama ruwansu yana malalowa daga Haikalin. 'Ya'yansu abinci ne, ganyayensu kuwa magani ne.”