Ezekiel 47:19 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A wajen kudu za tă fara daga Tamar har zuwa ruwan Meriba Kadesh, sa’an nan ta bi Rafin Masar zuwa Bahar Rum. Wannan ita ce iyakar a wajen kudu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«غَا يَدَّ إِيَاكَرْ كُدُ ذَاتَ كَسَنْثٜىٰ؞ إِيَاكَرْ ذَاتَ مِيڧٜىٰ ذُوَا يَمَّ دَغَ تَمَرْ تَبِے تَ ضُوً مٜىٰرِبَتْ كَدٜىٰشْ دَغَ ثَنْ ذَاتَبِے تَ رَاڢِنْ مَصَرْ حَرْ ذُوَا تٜىٰكُنْ مٜىٰدِتٜىٰرٜىٰنِيَ؞ وَنَّنْ عِتَثٜىٰ إِيَاكَ تَكُدُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“A wajen kudu, iyakar za ta kama daga Tamar har zuwa ruwan Meribakadesh, ta bi ta rafin Masar zuwa Bahar Rum. Wannan ita ce iyakar a wajen kudu.