Ezekiel 47:22 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Za ku raba ta kamar gādo wa kanku da kuma wa baƙin da suka zauna a cikinku waɗanda suke da ’ya’ya. Za ku ɗauka su kamar ’yan ƙasa haifaffun Isra’ilawa; za su yi gādo tare da ku a cikin kabilan Isra’ila.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ذَاكُ رَبَ ڧَسَرْ تَذَمَ مُكُ غَادُواْ، كُرَبَ أَڟَكَانِنْكُ دَ بَڧِنْ دَسُكٜىٰ ذَمَ عَثِكِنْكُ وَطَنْدَ سُكَ حَيْڢِ یَیَ عَثِكِنْكُ؞ ذَاسُ ذَمَ أَغَرٜىٰكُ كَمَرْ وَطَنْدَ عَكَ حَيْڢٜىٰسُ ثِكِنْ إِسْرَٰٓءِيلَ؞ ذَاعَبَاسُ رَبُوانْ غَادُوانْ ڧَسَرْ تَرٜىٰدَكُو ثِكِنْ ظُرِيُواْيِنْ إِسْرَٰٓءِيلَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Za ku raba ƙasar gādo a tsakaninku da baƙin da suke zaune tare da ku, waɗanda suka haifi 'ya'ya a cikinku. Za su zama kamar 'ya'yan Isra'ila haifaffu na gida. Za a ba su gādo tare da kabilan Isra'ila,