Ezekiel 47:3 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Yayinda mutumin ya yi wajen gabas da karan awo a hannunsa, sai ya auna kamu dubu ya kuma bi da ni ta ruwan da zurfinsa ya kama ni a idon ƙafa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَدَّ يَكٜىٰ نُڢَ تَغَبَسْ دَ إِغِيَ أَ حَنُّنْسَ يَنَ عَوْنَاوَا، يَكُوَ عَوْنَ كَمُ دُبُو طَيَ؞ بَايَنْ حَكَ يَبِے دَنِے مُكَ ڧٜىٰتَرٜىٰ ضُوً، ظُرْڢِنْ ضُوً كُوَ يَكَيْ عِدُوانْ ڧَڢَتَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Mutumin ya nufi wajen gabas da ma'auni a hannunsa, ya auna kamu dubu, sa'an nan ya sa ni in haye ruwan. Zurfin ruwan ya kama ni idon ƙafa.