Ezekiel 47:8 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai ya ce mini, “Wannan ruwa yana malalowa zuwa yankin gabas ya kuma gangaro zuwa cikin Araba, inda zai shiga Teku. Sa’ad da ya shiga cikin Tekun sai ruwan a can ya zama mai daɗi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَثٜىٰ مِنِ «وَنَّنْ ضُوَ ذَيْ غَنْغَرَ ذُوَا وَجٜىٰنْ غَبَسْ حَرْ ذُوَا ݣُورِنْ أَرَبَ نٜىٰ؞ سَعَدَّ يَشِغَ تٜىٰكُنْ غِشِرِ، ضُوً تٜىٰكُنْ كُوَ ذَيْ ثَنْجَ يَذَمَ ضُوَ مَيْ دَاطِے؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ya kuma ce mini, “Wannan ruwa yana gangarowa zuwa wajen gabas har zuwa cikin Araba. Zai shiga ruwan teku marar gudu, ruwan tekun kuwa zai zama ruwan daɗi.