Ezekiel 47:9 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Tarin halittu masu rai za su rayu a duk inda ruwan ya malalo. Za a kasance da kifi masu yawa, domin wannan ruwa yana malalowa a can yana kuma mai da ruwan gishiri yă zama ruwa mai daɗi; saboda haka duk inda ruwan ya malalo, kome zai rayu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دُكْ عِنْدَ كُواْغِنْ يَتَڢِے، كُواْوَثٜىٰ حَلِتَّ مَيْ رَيْ ذَاتَ رَايُ؞ ذَاعَ سَامِ كِيڢَيٜىٰ دَيَوَ عَثِكِ، مُدِّنْ ضُوًنَنْ يَكَيْ ثِكِنْ ضُوً تٜىٰكُ؞ ضُوً ذَيْ ثَنْجَ يَذَمَ ضُوَ مَيْݣَوْ؞ دُكْ عِنْدَ ضُوًنَنْ يَتَڢِے كُواْوَنٜىٰ أَبُ ذَيْ رَايُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Kowace halitta mai rai da take cikin wannan ruwa za ta rayu. Za a sami kifaye da yawa a ciki, domin wannan ruwa zai kai wurin ruwan tekun, zai kuwa zama ruwan daɗi. Duk inda ruwan nan ya tafi kowane abu zai rayu.