Ezekiel 48:10 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Wannan ne zai zama tsattsarkan rabo domin firistoci. Tsawon zai zama kamu 25,000 a wajen arewa, fāɗin kuma kamu 10,000 wajen yamma, kamu 10,000 zai zama fāɗinsa a wajen gabas, tsawonsa a wajen kudu zai zama kamu 25,000. A tsakiyarsa ne wuri mai tsarki na Ubangiji zai kasance.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
وَنَّنْ سَاشٜىٰنْ دَ عَكَ كٜىٰٻٜىٰ دَ ڟَرْكِے ذَيْ ذَمَ رَبُوانْ ڢِرِسْتُواْثِے؞ ڟَوُانْسَ أَغٜىٰڢٜىٰنْ أَرٜىٰوَ ذَيْ ذَمَ كَمُ دُبُو عَشِرِنْ دَ بِيَرْ، ڢَاطِنْسَ أَغٜىٰڢٜىٰنْ يَمَّ ذَيْ ذَمَ كَمُ دُبُو غُواْمَ، أَغٜىٰڢٜىٰنْ غَبَسْ كُمَ ڢَاطِنْسَ ذَيْ ذَمَ كَمُ دُبُو غُواْمَ، أَغٜىٰڢٜىٰنْ كُدُ كُمَ ڟَوُانْسَ ذَيْ ذَمَ كَمُ دُبُو عَشِرِنْ دَ بِيَرْ؞ وُرِے مَيْ ڟَرْكِے نَ يَهْوٜىٰهْ ذَيْ كَسَنْثٜىٰ أَڟَكِيَرْ سَاشٜىٰنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Wannan tsattsarkan yanki shi ne rabon firistoci. Tsawonsa wajen arewa, kamu dubu ashirin da dubu biyar [25,000] ne, faɗinsa a wajen yamma kuwa, kamu dubu goma [10,000] ne, a wajen gabas faɗinsa kamu dubu goma [10,000], a wajen kudu tsawonsa kamu dubu ashirin da dubu biyar [25,000]. Haikalin Ubangiji zai kasance a tsakiyarsa.