Ezekiel 48:17 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Wurin kiwo don birnin zai zama kamu 250 a wajen arewa, kamu 250 a wajen kudu, kamu 250 a wajen gabas da kuma kamu 250 a wajen yamma.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
غَا يَدَّ ڢِيلِنْ كِيوُاْ نَبِرْنِنْ ذَيْ كَسَنْثٜىٰ؞ أَغٜىٰڢٜىٰنْ أَرٜىٰوَ كَمُ طَرِے بِيُ دَ حَمْسِنْ، أَغٜىٰڢٜىٰنْ كُدُ كَمُ طَرِے بِيُ دَ حَمْسِنْ، أَغٜىٰڢٜىٰنْ غَبَسْ كَمُ طَرِے بِيُ دَ حَمْسِنْ، أَغٜىٰڢٜىٰنْ يَمَّ كُمَ كَمُ طَرِے بِيُ دَ حَمْسِنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Birnin zai kasance da hurumi a kewaye da shi. A wajen gabas kamu metan da hamsin, a wajen yamma kamu metan da hamsin, a wajen kudu kamu metan da hamsin, a wajen arewa kuma kamu metan da hamsin.