Ezekiel 48:18 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Tsawon abin da ya rage a wurin, dab da tsattsarkan rabo, zai zama kamu 10,000 wajen gabas, kamu 10,000 kuma wajen yamma. Amfanin da zai bayar zai tanada abinci don ma’aikatan birnin.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ضَغُواْوَرْ سَاشٜىٰنْ بِيٜىٰ دَ سَاشٜىٰنْ دَ عَكَ كٜىٰٻٜىٰ دَ ڟَرْكِے، ذَاتَ ذَمَ كَمُ دُبُو غُواْمَ أَغٜىٰڢٜىٰنْ غَبَسْ دَ كَمُ دُوبَ غُواْمَ أَغٜىٰڢٜىٰنْ يَمَّ؞ ڟَوُانْتَ ذَيْبِے ڟَوُانْ سَاشٜىٰنَّنْ دَ عَكَ كٜىٰٻٜىٰ؞ أَمْڢَانِنْ دَ ذَاعَ سَامُ دَغَ سَاشٜىٰنَّنْ، ذَيْ ذَمَ نَمَعَيْكَتَنْ بِرْنِنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ragowar tsawon yankin da yake gab da tsattsarkan yankin, zai zama kamu dubu goma [10,000] a wajen gabas, a wajen yamma kamu dubu goma [10,000]. Amfanin da yankin zai bayar, zai zama abincin ma'aikatan birnin.