Ezekiel 48:21 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Abin da ya rage a kowane gefe na wurin zai zama tsattsarkan rabo kuma mallakar birnin za tă zama ta sarki. Zai miƙe wajen gabas daga kamu 25,000 na tsattsarkan rabo zuwa iyakar da take wajen gabashin iyaka, da kuma a wajen yamma kamu 25,000 zuwa iyakar da take a wajen yamma. Dukan wuraren nan da suke hannun riga da rabon kabilan zai zama na sarki, tsattsarkan rabon tare da wuri mai tsarkin za su kasance a tsakiyarsu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«دُكَنْ ضَغُواْوَرْ سَاشٜىٰ بِيٜىٰ دَ كُواْوَنٜىٰ غٜىٰڢٜىٰ نَسَاشٜىٰنْ دَ عَكَ كٜىٰٻٜىٰ دَ ڟَرْكِے تَرٜىٰدَ سَاشٜىٰ نَبِرْنِنْ ذَيْ ذَمَ نَسَرْكِے؞ ذَيْ مِيڧٜىٰ غَبَسْ دَغَ سَاشٜىٰ مَيْ كَمُ دُبُو عَشِرِنْ دَ بِيَرْ نَسَاشٜىٰنْ وُرِے مَيْ ڟَرْكِے ذُوَا إِيَاكَرْ ڧَسَرْ أَغٜىٰڢٜىٰنْ غَبَسْ؞ ذَيْ كُمَ مِيڧٜىٰ يَمَّ دَغَ سَاشٜىٰ مَيْ كَمُ دُبُو عَشِرِنْ دَ بِيَرْ نَسَاشٜىٰنْ وُرِے مَيْ ڟَرْكِے ذُوَا إِيَاكَرْ ڧَسَرْ أَغٜىٰڢٜىٰنْ يَمَّ؞ دُكَنْ وُرَارٜىٰنَّنْ بِيُ وَطَنْدَ سُكَبِے تَغٜىٰڢٜىٰنْ سَاشٜىٰنْ ظُرِيُواْيِ ذَاسُ ذَمَ نَسَرْكِے؞ سَشٜىٰنْ دَ عَكَ كٜىٰٻٜىٰ دَ ڟَرْكِے تَرٜىٰدَ هَيْكَلِنْ ذَاسُ كَسَنْثٜىٰ أَڟَكِيَرْسُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Ragowar kowane gefe na tsattsarkan yankin da hurumin birnin, zai zama na sarki. Tun daga kamu dubu ashirin da dubu biyar [25,000] na tsattsarkan yankin, zuwa iyakar da take wajen gabas, daga kamu dubu ashirin da dubu biyar [25,000] kuma zuwa iyakar wajen yamma, hannun riga da yankunan kabilan zai zama na sarki. Tsattsarkan yankin da wuri mai tsarki na Haikali za su kasance a tsakiyarsa.