Ezekiel 48:8 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Kusa da yankin Yahuda daga gabas zuwa yamma zai zama rabon da za ku bayar a matsayin kyauta ta musamman. Faɗinsa zai zama kamu 25,000, tsawonsa kuma zai zama daidai da tsawon yankunan kabilu daga gabas zuwa yamma; wuri mai tsarki zai kasance a tsakiyar wannan yanki.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«بِيٜىٰ دَ سَاشٜىٰنْ ذُرِيَرْ يَهُودَ، إِيَاكَرْ ذَاتَ مِيڧٜىٰ دَغَ غَبَسْ ذُوَا يَمَّ؞ ذَاعَكٜىٰٻٜىٰ سَاشٜىٰنَّنْ يَذَمَ ݣَوْتَا تَمُسَمَّنْ؞ ڢَاطِنْسَ ذَيْ كَمُ دُبُو عَشِرِنْ دَ بِيَرْ، ڟَوُانْسَ كُمَ دَيْدَيْ دَ ڟَوُانْ رَبُوانْ غَادُواْ نَسَاشٜىٰنْ ذُرِيَ طَيَ وَنْدَ يَمِيڧٜىٰ دَغَ غَبَسْ ذُوَا يَمَّ؞ وُرِے مَيْ ڟَرْكِے كُمَ ذَيْ كَسَنْثٜىٰ أَڟَكِيَرْ سَاشٜىٰنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Kusa da yankin Yahuza daga gabas zuwa yamma, sai yankin da za ku keɓe. Faɗinsa kamu dubu ashirin da dubu biyar [25,000], tsawonsa kuma daidai da tsawon yankunan kabilai daga gabas zuwa yamma. Haikali zai kasance a tsakiyar yankin.