Ezekiel 5:11 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Saboda haka muddin ina a raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, domin kin ƙazantar da wuri mai tsarkina da dukan mugayen siffofinki da kuma ayyukanki masu banƙyama, ni kaina zan janye alherina; ba zan ji tausayinki ko in haƙura da ke ba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«دُواْمِنْ وَنَّنْ، إِنْجِنِ عُبَنْغِجِ يَهْوٜىٰهْ نَا ضَنْڟٜىٰ دَ رَيْنَ، حَڧِيڧَ تُنْدَ كِكَ ڧَظَنْتَرْدَ وُرِنْ ذَمَنَ مَيْ ڟَرْكِے تَوُرِنْ أَبُبُوَنْكِ نَڧَظَنْتَا، تَرٜىٰدَ أَبُبُوَ مَاسُ بَنْ ڨَمَرْ نَنْ، ذَنْ كَوَرْ دَكٜىٰ؞ بَذَنْ بَرْ كِبَ، بَكُوَ ذَنْجِے تَوْسَيِنْكِبَ كُواْ كَطَنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“‘Tun da yake kin ƙazantar da Haikalina mai tsarki da gumakanki da abubuwanki masu banƙyama, hakika, ni Ubangiji Allah, zan kawar da ke, ba zan ji tausayinki ba, ba kuwa zan haƙura ba.