Ezekiel 5:4 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Har yanzu, ka ɗibi kaɗan na waɗannan ka zuba su cikin wuta su kuma ƙone. Wuta zai bazu daga nan zuwa dukan gidan Isra’ila.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَغَ ثِكِنْ غَاشِنَّنْ كُمَ، ذَاكَسَاكٜىٰ طِبَ كَطَنْ كَجٜىٰڢَسُ عَثِكِنْ وُتَا؞ دَغَ نَنْ نٜىٰ وُتَا ذَاتَ تَاشِ عَكَنْ دُكَنْ غِدَنْ إِسْرَٰٓءِيلَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Daga cikin gashi kaɗan ɗin nan kuma, sai ka ɗibi waɗansu ka sa a wuta. Daga nan ne wuta za ta tashi a Isra'ila duka.”