Ezekiel 6:13 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Za su kuwa san cewa ni ne Ubangiji, sa’ad da gawawwakin mutanensu suna kwance a kusa da gumakansu da kewaye da bagadansu, a kowane kan tudu mai tsawo da kuma a kan dukan kan duwatsu, a ƙarƙashin kowane inuwar itace da kuma kowane oak mai ganye, wuraren da suke ƙone turare masu ƙanshi wa dukan gumakansu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ذَاكُسَنِ ثٜىٰوَ نِنٜىٰ يَهْوٜىٰهْ ، سَعَدَّ غَوَوَّكِنْسُ سُنْ ݣُونْتَ تَرٜىٰدَ غُمَكَنْسُ كٜىٰوَيٜىٰ دَ بَغَدَنْسُ دَ كَنْ كُواْوَنٜىٰ تُدُ مَيْ ڟَيِ دَ سَمَنْ دُكَنْ مَنْيَنْ تُدَّيْ دَ عَڧَرْڧَشِنْ كُواْوَنٜىٰ إِتَاثٜىٰ مَيْ بَادَ إِنُوَ دَ عَڧَرْڧَشِنْ كُواْوَنٜىٰ إِتَاثٜىٰنْ ڟَاڢِ مَيْ غَنْيٜىٰ دَ كُمَ دُكْ عِنْدَ سُكَ مِيڧَ تُرَارٜىٰ مَيْ ڧَنْشِ غَ دُكَنْ غُمَكَنْسُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Za ku kuwa sani ni ne Ubangiji, sa'ad da gawawwakinsu sun kwanta tare da gumakansu kewaye da bagadansu a kan kowane tudu, da kan tsaunuka, da ƙarƙashin kowane itace mai duhuwa, da ƙarƙashin itacen oak mai ganye, duk inda suka miƙa turare mai ƙanshi ga dukan gumakansu.