Ezekiel 6:9 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’an nan a cikin al’ummai inda aka kai ku zaman bauta, waɗanda suka a tsere za su tuna da ni, yadda raina ya ɓaci ta wurin zukatansu marasa imani, waɗanda suka rabu da ni, da kuma ta wurin idanunsu, waɗanda suka yi sha’awace-sha’awacen gumakansu. Za su ji ƙyamar kansu saboda mugayen abubuwan da suka aikata.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
وَطَنْدَ سُكَ ڟِيرَا ذَاسُ تُنَ دَنِے عَثِكِنْ أَلْعُمَّيْ عِنْدَ عَكَ كَيْسُ بَوْتَا؞ ذَاسُ كُمَ تُنَ يَدَّ رَيْنَ يَٻَثٜىٰ سَبُواْدَ ذُوثِيَارْسُ تَ رَشِنْ أَمِنْثِ وَدَّ تَسَا سُكَ جُويَا دَغَ غَرٜىٰنِ دَ يَدَّ عِدَنُونْسُ نَشَعَوَ سُكَسَاسُ سُبِے غُمَكَنْسُ؞ ذَاسُ كُوَجِ ڨَمَرْ كَنْسُ سَبُواْدَ دُكَنْ مُغُنْتَارْ دَسُكَ عَيْكَتَ دَ كُمَ دُكَنْ أَيُّكَنْ ڧَظَنْتَرْسُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Waɗansunku da suka tsere za su tuna da ni cikin al'ummai inda aka kai su bautar talala yadda raina ya ɓaci saboda zuciyarsu ta rashin imani wadda ta rabu da ni, da idanunsu masu zina da suke bin gumaka. Za su kuwa ji ƙyamar kansu saboda mugayen abubuwa da suka aikata.