Ezekiel 7:20 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sun yi fariya kyan kayan adonsu suka kuma yi amfani da su don su yi gumakansu masu banƙyama, da ƙazantattun abubuwa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ݣَوَوَنْ كَايَنْ أَدُوانْسُ يَسَا سُطَغَ كَيْ، دَ كَايَنَّنْ سُكَيِ صِڢُّواْڢِ مَاسُ بَنْ ڨَمَ، دَ أَبُبُوَ مَاسُ ڧَظَنْتَا؞ سَبُواْدَ حَكَ ذَنْ مَيْدَ كَايَنَّنْ أَبِنْ ڧَظَنْتَا أَغَرٜىٰسُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Suna fariyar banza da kyawawan kayan adonsu, na zinariya da azurfa. Da su suka yi siffofi masu banƙyama, da ƙazantattun abubuwa. Domin haka zan maishe su ƙazantattun abubuwa a gare su.