Ezekiel 7:4 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ba zan dube ki da tausayi; ko in ƙyale ki ba. Tabbatacce zan sāka miki saboda halinki da kuma ayyukanki masu banƙyama a cikinki. Sa’an nan za ki san cewa ni ne Ubangiji.’
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بَذَنْ بَرْ كِبَ، بَ كُوَ ذَنْجِے تَوْسَيِنْكِبَ؞ ذَنْ حُكُنْتَكِ بِسَغَ هَنْيُواْيِنْكِ، بِسَغَ أَبُبُوَنْ بَنْ ڨَمَرْ دَ كِكَ عَيْكَتَ؞ سَعَنً نٜىٰ ذَاكِ سَنِ ثٜىٰوَ نِنٜىٰ يَهْوٜىٰهْ ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ba zan yafe miki ba, ba kuwa zan ji tausayinki ba, amma zan hukunta ki saboda ayyukanki sa'ad da kike tsakiyar aikata ƙazantarki. Sa'an nan za ki sani ni ne Ubangiji.”