Ezekiel 8:11 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A gabansu ga dattawa saba’in na gidan Isra’ila tsaye a cikinsu, Ya’azaniya ɗan Shafan kuwa yana tsaye a cikinsu. Kowa yana da farantin ƙona turare a hannunsa, tulin hayaƙin turare mai ƙanshi ya tunnuƙe zuwa sama.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَغَبَنْسُ أَݣَويْ دَتَّاوَا سَبَعِنْ نَغِدَنْ إِسْرَٰٓءِيلَ أَڟَيٜىٰ؞ عَڟَكِيَرْسُ كُمَ يَعَظَنِيَ طَنْ شَڢَنْ يَنَ أَڟَيٜىٰ؞ كُواْوَنٜىٰ طَيَ دَغَ ثِكِنْ شُوغَبَنِّنْ يَنَ رِڧٜىٰ دَ ڢَرَنْتِنْ تُرَارٜىٰ أَ حَنُّنْسَ، هَيَاڧِنْ تُرَارٜىٰنْ يَنَ تَاشِ سَمَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Dattawan Isra'ila saba'in suna tsaye a gabansu. Yazaniya ɗan Shafan yana tsaye tare da su. Kowa yana riƙe da farantin ƙona turare. Hayaƙin turaren ya tunnuƙe zuwa sama.