Ezekiel 8:2 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Na duba, sai na ga siffa kamar na mutum. Daga kwankwaso zuwa ƙasa ya yi kamar wuta, kuma daga kwankwaso zuwa sama kamanninsa ya yi haske yana ƙyalli kamar ƙarfe mai haske.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَدَّ نَكٜىٰ كَلُّواْ، سَيْ نَغَ صِڢَّ وَدَّ تَيِ كَمَ دَ كَمَنِّنْ مُتُمْ؞ دَغَ ݣُونْݣُوسُوانْ صِڢَّرْ ذُوَا ڧَسَا يَنَدَ كَمَنِّنْ وُتَادَغَ ݣُونْݣُوسُوانْتَ ذُوَا سَمَ يَنَ ڨَلِّ كَمَرْ تَغُلَّرْ دَ عَكَ غُواْغٜىٰ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Da na duba, sai ga siffa wadda dake da kamannin mutum. Daga kwankwason siffar zuwa ƙasa yana da kamannin wuta, daga kwankwason kuma zuwa sama yana da haske kamar na tagulla.