Ezekiel 9:2 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Na kuma ga mutane shida suna zuwa daga kowane gefen ƙofar ta bisa, wadda take fuskantar arewa, kowanne da makamin kisa a hannunsa. Tare da su akwai mutum saye da lilin yana rataye da jaka ƙunshe da kayan rubutu a gefensa. Suka shiga suka tsaya kusa da bagaden tagulla.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
غَا مُتُمْ شِدَ سُكَ ڢِتُواْ دَغَ وَجٜىٰنْ ڧُواْڢَرْ غِدَنْ اللَّهْ وَدَّ تَكٜىٰ أَوُرِے مَڢِے ڟَيِ تَنَ ڢُسْكَنْتَرْ أَرٜىٰوَ، كُواْوَنّٜىٰنْسُ دَ مَكَامِنْسَ نَهَلَّكَرْوَ أَ حَنُّ؞ عَڟَكِيَرْسُ أَݣَويْ وَنِ مُتُمْ سَنْيٜىٰ دَ رِغَرْ لِيلِنْ، يَنَ كُمَ رَاتَيٜىٰ دَ أَبِنْ رُبُوتُو أَغٜىٰڢٜىٰنْسَ؞ سَيْ سُكَ شِغَ، سُكَ ڟَيَ أَغٜىٰڢٜىٰنْ بَغَدٜىٰنْ تَغُلَّ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai ga mutum shida sun taho daga wajen ƙofa wadda take daga bisa wadda ta fuskanci arewa. Kowa yana da makaminsa na kisa a hannu. Tare da su kuma akwai wani mutum saye da rigar lilin, yana kuma rataye da gafaka. Sai suka tafi suka tsaya a gefen bagaden tagulla.