Ezra 1:11 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Dukan kayayyakin zinariya da na azurfa sun kai 5,400. Sheshbazzar ya kawo kayayyakin nan duka tare da shi lokacin da kamammun suka hauro daga Babilon zuwa Urushalima.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دُكَنْ كَايَيَّكِ نَظِينَارِيَ دَ نَأَظُرْڢَا سُنْ كَيْ دُبُو بِيَرْ دَ طَرِے حُطُ؞ شٜىٰشْبَظَّرْ يَهَوْرُواْ دَ دُكَنْ وَطَنَّنْ كَايَيَّكِ سَعَدَّ وَطَنْدَ دَا عَكَ كَيْسُ بَوْتَا سُكَ هَوْرَ دَغَ بَابِيلَ ذُوَا عُرُوشَلِيمَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Jimillar kayayyakin duka, na zinariya da na azurfa, dubu biyar da arbaminya (5,400). Sheshbazzar ya tafi da waɗannan kayayyaki duka tare da kamammun da suka komo daga Babila.