Ezra 1:4 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Duk inda akwai mutumin Yahuda da ya rage, sai mutanen da suke zama kusa da shi, su taimake shi da azurfa, da zinariya, da kaya, da kuma dabbobi, tare da kyautai na yardar rai saboda Gidan Allah wanda yake a Urushalima.’ ”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دُكْ عِنْدَ أَݣَويْ مُتُمِنْ يَهُودَ دَ يَرَغُ، سَيْ مُتَنٜىٰنْ دَسُكٜىٰ ذَمَ كُسَدَشِ، سُتَيْمَكٜىٰشِ دَ أَظُرْڢَا دَ ظِينَارِيَ دَ كَايَ دَ كُمَ دَبُّواْبِے، تَرٜىٰدَ بَيٜىٰ بَيٜىٰنْكُ نَيَرْدَرْ رَيْ سَبُواْدَ غِدَنْ اللَّهْ وَنْدَ يَكٜىٰ أَ عُرُوشَلِيمَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A duk inda akwai wani Bayahude, sai mutanen wurin su taimake shi da azurfa, da zinariya, da kaya, da dabbobi, tare da waɗansu kyautai na yardar rai saboda Haikalin Ubangiji wanda yake a Urushalima.”