Ezra 1:6 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Dukan maƙwabtansu kuwa suka taimake su da gudummawa na kayan azurfa da na zinariya, da kaya, da dabbobi, da kuma kyautai masu daraja bisa bayarwar yardar rai da suka yi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دُكَنْ وَطَنْدَ سُكٜىٰ ذَمَ كُسَدَ يَهُودَاوَا، سُكَ تَيْمَكٜىٰسُ دَ كَايَنْ دَ عَكَيِ دَ أَظُرْڢَا دَ ظِينَارِيَ دَ وَطَنْسُ كَايَ دَ دَبُّواْبِے، تَرٜىٰدَ أَبُبُوَ مَاسُ دَرَجَ بَنْدَ ݣَوْتَيْ نَيَرْدَرْ رَيْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Dukan waɗanda suke kewaye da su, suka taimake su da azurfa, da zinariya, da kayayyaki, da dabbobi, da abubuwa masu daraja, da kyautai na yardar rai.