Ezra 10:14 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Bari shugabanninmu su yi wani abu a madadin mutane duka, sa’an nan sai duk wanda ya san ya auri baƙuwar mace a garuruwanmu, sai yă zo nan a lokacin da aka shirya tare da dattawa da alƙalan kowane gari, har sai Allah ya huce fushinsa mai zafi da yake kanmu.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بَرِ شُوغَبَنِّنْمُ سُكَسَنْثٜىٰ أَ عُرُوشَلِيمَ سُدُوبِے أَلْعَمَرِنْ أَمَدَدِنْ دُكَنْ تَارُوانْ جَمَعَرْ؞ سَعَنً دُكَنْ مُتَنٜىٰنْ غَرُرُوَنْمُ وَطَنْدَ سُكَ عَوْرِ مَاتَانْ بَاڧِ دَغَ ڧَبِيلُنْ دَ بَا يَهُودَاوَا بَ، سُذُواْ أَدَيْدَيْ لُواْكَثِنْ دَ عَكَسَا مُسُ، تَرٜىٰدَ دَتَّاوَا دَ أَلْڧَلَيْ نَكُواْوَنٜىٰ غَرِ؞ ذَامُيِ حَكَ دُواْمِنْ اللَّهْ نْمُ يَهُوثٜىٰ دَغَ ڢُشِنْسَ مَيْ ذَاڢِ عَكَنْ وَنَّنْ أَلْعَمَرِ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Bari shugabanninmu su wakilci dukan taron jama'a, bari kuma dukan waɗanda suke garuruwanmu da suka auri mata baƙi su zo a ƙayyadadden lokaci tare da dattawa da alƙalan garuruwansu, har lokacin da Allah ya huce daga fushinsa a kanmu saboda al'amarin nan.”