Ezra 10:9 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A cikin kwana uku duk mutanen Yahuda da na Benyamin suka taru a Urushalima. A ranar ashirin ga watan tara, dukan mutanen suka zauna a dandali a gaban gidan Allah cike da ɓacin rai saboda abin da ya faru da kuma ruwan da aka yi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
كَاڢِنْ ݣُونَ عُكُنَّنْ دُكَنْ مَذَنْ دَسُكٜىٰ ذَمَ عَيَنْكِنْ يَهُودَ دَ نَ بِلِيَامِنُ سُكَ تَارُ أَ عُرُوشَلِيمَ؞ أَ رَانَ تَعَشِرِنْ غَ وَتَنْ تَرَ دُكَنْ مُتَنٜىٰ سُكَ ظَظْذَوْنَ عَثِكِنْ ڢِيلِنْ دَيَكٜىٰ أَغَبَنْ غِدَنْ اللَّهْ ؞ سَبُواْدَ مُهِمَّنْثِنْ وَنَّنْ أَلْعَمَرِ دَ كُمَ ڟَنَنِنْ ضُوً سَمَنْ دَ عَكٜىٰيِ، كُواْوَ يَيِ تَرَوَرْ جِكِے؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai dukan mutanen Yahuza da na Biliyaminu, suka hallara a Urushalima kafin kwana uku, a ran ashirin ga watan tara. Mutanen suka zauna a dandalin Haikali, suna rawar jiki saboda al'amarin, da kuma saboda babban ruwan sama.