Ezra 3:11 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Suka rera waƙar yabo da godiya ga Ubangiji, suna cewa, “Shi nagari ne; ƙaunarsa kuwa ga Isra’ila har abada ce.” Dukan jama’a kuwa suka yabi Ubangiji da murya mai ƙarfi, domin an aza harsashin ginin gidan Ubangiji.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
وَطَنْسُ سُكَ طَغَ وَاڧَرْ غُواْدِيَ دَ يَبُواْ غَ يَهْوٜىٰهْ ، وَطَنْسُ سُنَ أَمْسَاوَا سُنَ ثٜىٰوَ «غَمَا يَهْوٜىٰهْ مَيْ أَلْحٜىٰرِ نٜىٰ، ڧَوْنَرْسَ مَرَرْ ثَنْجَاوَا تَهَرْ أَبَدَا ثٜىٰ غَ إِسْرَٰٓءِيلَ؞» سَيْ دُكَنْ مُتَنٜىٰ سُكَتَادَ مُرْيَ دَ ڧَرْڢِے سُكَ يَبِے يَهْوٜىٰهْ سَبُواْدَ أَنْكَڢَ تُوشٜىٰنْ غِدَنْ يَهْوٜىٰهْ ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Da bangirma suka raira waƙa ta yabo da godiya ga ubangiji, suna cewa, “Ubangiji nagari ne, Gama ƙaunarsa marar matuƙa ce, Ta tabbata har abada ga Isra'ila.” Sai mutane duka suka ɗaga murya da ƙarfi suka yabi Ubangiji, saboda an aza harsashin ginin Haikalin Ubangiji.