Ezra 3:12 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Amma tsofaffin firistoci, da Lawiyawa, da shugabannin iyalai da yawa, waɗanda dā suka ga yadda haikali na farko yake, suka fashe da kuka mai ƙarfi sa’ad da suka ga an aza harsashin ginin wannan haikali, yayinda waɗansu kuma suka yi ihu da farin ciki.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَمَّا دَيَوَ دَغَ ثِكِنْ ڟُواْڢَڢِّنْ مُتَنٜىٰ، ڢِرِسْتُواْثِے دَ لَوِيَاوَا دَ شُوغَبَنِّنْ دَنْغِ دَنْغِ، وَطَنْدَ دَا سُكَغَ غِدَنْ يَهْوٜىٰهْ نَڢَرْكُواْ، سُكَ ڢَشٜىٰ دَ كُوكَا مَيْ ذَاڢِ، سَعَدَّ سُكَغَ تُوشٜىٰنْ وَنَّنْ غِدَنْ؞ وَطَنْسُ كُوَ سُكَتَادَ مُرْيَ دُواْمِنْ ڢَضٍ ثِكِ،
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Amma da yawa daga cikin firistoci, da Lawiyawa, da shugabannin gidajen kakanni, wato tsofaffi waɗanda suka ga Haikali na farko, suka yi kuka da babbar murya a sa'ad da suka ga an aza harsashin ginin wannan Haikali. Waɗansu kuwa suka yi sowa don farin ciki.