Ezra 3:6 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A ranar farko ta watan bakwai, sai suka fara miƙa hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji, ko da yake ba a riga an aza harsashin ginin haikalin Ubangiji ba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
تُنْدَغَ رَانَ تَڢَرْكُواْ غَ وَتَنْ بَݣَويْ سُكَ ڢَارَ مِيڧَ هَدَايُ نَڧُواْنَاوَا غَ يَهْوٜىٰهْ ، كُواْدَيَكٜىٰ بَعَكَڢَ تُوشٜىٰنْ هَيْكَلِنْ يَهْوٜىٰهْ بَ تُكُنَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Tun daga rana ta fari ga watan bakwai, suka fara miƙa wa Ubangiji hadayu na ƙonawa, amma ba a riga an aza harsashin Haikalin Ubangiji ba.