Ezra 4:12 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ya kamata sarki ya san cewa Yahudawan da suka hauro wurinmu daga wurinka, sun je Urushalima suna sāke gina wannan mugun birni mai tawaye. Suna sāke gyara katangar, suna kuma gyara harsashin katangar.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«مُنَ سُواْ مَيْغِرْمَ سَرْكِے يَسَنِ ثٜىٰوَ يَهُودَاوَنَّنْ وَطَنْدَ سُكَ هَوْرُواْ دَغَ وُرِنْكَ ذُوَا عِنْدَ مُكٜىٰ سُنْ تَڢِے عُرُوشَلِيمَ؞ سُنَ سَاكٜىٰ غِنَا مُوغُنْ بِرْنِنَّنْ نَتَاوَيٜىٰ؞ سُنَ ڧَارَسَ غِنِنْ كَتَنْغَرْ، سُنَ ڠَرٜىٰ ڠَرٜىٰنْ تُوشٜىٰنْ دَ سَوْرَنْ بِرْنِنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Muna sanar da sarki, cewa Yahudawan nan waɗanda suka fito daga gare ka suka zo wurinmu, sun tafi Urushalima, suna sāke gina mugun birnin nan na tawaye, sun fara gina garun, ba da jimawa ba za su gama ginin.