Ezra 4:23 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Da gama karanta wasiƙar sarki Artazerzes wa Rehum da Shimshai marubuci, da abokansu, sai suka yi sauri suka je wurin Yahudawa a Urushalima, suka hana su aikin ƙarfi da yaji.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَظَرَرْ عَكَ كَرَنْتَ وَسِيڧَ تَسَرْكِے أَرْتَظٜىٰكْظٜىٰسْ أَغَبَنْ رٜىٰهُمْ دَ شِمْشَيْ مَرُبُوثِ دَ سَوْرَنْ أَبُواْكَنْسُ، سَيْ سُكَيِ سَوْرِ ذُوَا وُرِنْ يَهُودَاوَا أَ عُرُوشَلِيمَ، سُكَ هَنَاسُ عَيْكِنْ ڧَرْڢِے دَ يَجِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'ad da aka karanta wa Rehum, da Shamshai magatakarda, da abokansu, wasiƙar sarki Artashate, suka hanzarta suka tafi wurin Yahudawa a Urushalima, suka gwada musu iko, suka tilasta musu su daina ginin.