Ezra 5:17 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Yanzu in sarki yana so, bari a duba cikin littattafan tarihi na sarakuna na Babilon a gani ko lalle sarki Sairus ya ba da umarni a sāke gina gidan Allah a Urushalima. Bari sarki yă aiko mana da abin da ya gani game da wannan abu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«سَبُواْدَ حَكَ عِدَنْ يَا غَمْشِ سَرْكِے، بَرِ عَيِ بِنْثِكٜىٰ ثِكِنْ طَاكِنْ لِتَّتَّڢَنْ تَارِيحِ نَ بَابِيلَ، كُواْ أَݣَويْ عُمَرْنِنْ دَ سَرْكِے سَيِرُسْ يَرُبُوتَ وَنْدَ يَبَادَ إِظْنِ أَ سَاكٜىٰ غِنَا وَنَّنْ غِدَنْ اللَّهْ أَ عُرُوشَلِيمَ، كُواْ كُوَ بَابُ؞ بَرِ كُمَ سَرْكِے يَعَيْكُواْ مَنَ دَ رَعَيِنْسَ عَكَنْ وَنَّنْ ذَنْثٜىٰنْ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Domin haka in ya gamshi sarki, sai a bincike ɗakin littattafan da yake Babila don a gani ko sarki Sairus ya ba da izini a sāke gina wannan Haikalin Allah a Urushalima. Bari sarki ya aiko mana da abin da ya gani a kan wannan al'amari.”