Ezra 5:6 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ga wasiƙar da Tattenai, gwamnan Kewayen Kogin Yuferites, da Shetar-Bozenai da abokansu masu riƙe da muƙamai a Kewayen Kogin Yuferites suka aika wa Sarki Dariyus.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
غَا أَبِنْدَ يَكٜىٰ عَثِكِنْ وَسِيڧَرْ دَ تَتّٜىٰنَيْ، ڠُومْنَنْ يَنْكِنْ ڧٜىٰتَرٜىٰنْ كُواْغِنْ يُڢِرٜىٰتِسْ دَ شٜىٰتَرْ بُواْظٜىٰنَيْ دَ أَبُواْكَنْسُ دَسُكٜىٰ دَتَّاوَنْ يَنْكِنْ ڧٜىٰتَرٜىٰنْ كُواْغِنْ يُڢِرٜىٰتِسْ سُكَ عَيْكَ وَ سَرْكِے دَرِيُسْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Wannan ita ce wasiƙar da Tattenai mai mulkin lardin Yammacin Kogi, da Shetar-bozenai, da abokansu ma'aikatan hukuma waɗanda suke Yammacin Kogi, suka aika wa sarki Dariyus.